<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>316</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Duba taron nan mai girma
 Wanda ba mai ƙirgawa,
 Suna tsaye gaban Allah,
 Suna yabon sunansa.
 Suna rera sabuwar waƙa,
 Suna ta da murya,
 Mulki, iko, girma, yabo,
 Naka ne har abada.

[V2]
 2) Su waɗanda suka fito
 Daga cikin tsanani,
 Suka wanke tufafinsu
 Cikin jinin Almasihu,
 Suka jure, babu tsoro,
 Suka raina mutuwa,
 Sun ci nasara kan Shaiɗan
 Cikin ƙarfin Ahmasihu.

[V3]
 3) Domin wannan, gaban Allah,
 Yafaffu da cetonsa,
 Suna yi masa sujada
 Kullum, ba mai fasawa.
 Yunwa, ba sa jinta kuma,
 Yesu yana kiwonsu,
 Shi ya shafe hawayensu
 Daga dukan idanu.

[V4]
 4) Almasihu, muna roƙo,
 Ubangijin tsarkaka,
 Taimake mu cikin duniya
 Mu bi sawun shaidunka.
 Haka za mu ratsa mutuwa,
 Za mu shiga mulkinka,
 Inda Masu Binka duka
 Su ke yabon ƙaunarka.</lyrics>
<title>Duba Taron Nan Mai Girma LW316</title>
</song>